Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Soja Ta Yankewa Wasu Sojoji Hukuncin Dauri


Birgediya Janar Olusegun Adeniyi shugaban kotun sojan dake Maiduguri
Birgediya Janar Olusegun Adeniyi shugaban kotun sojan dake Maiduguri

Jiya wata kotun soja a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno ta yankewa wasu sojoji biyu hukuncin dauri saboda ta same su da laifuka da aka zargesu da aikatawa

Birgediya Janar Olusegun Adeniyi shi ne shugaban kotun wanda ya yanke ma sojojin biyu hukuncin dauri a gidan kaso.

Kotun ta yankewa Hassan Adamu hukuncin shekaru bakwai a gidan kaso sakamakon laifin kisa da aka sameshi dashi amma kuma ba da gangan ba. An zargeshi da aikata laifin ne ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2015 sakamakon durkawa wani Umar Aka harsashai har sau biyu a kirjinsa a bakin kasuwar Litinin ko Monday Market. Nan take Umar Aka ya bar duniya.

Shugaban kotun yace kotun ta sameshi da laifin kisa ba da gangan ba maimakon kisa da gangan. Dalili ke nan da aka yanke masa hukuncin shekaru bakwai maimakon hukuncin kisa. Amma sai hukumomin soja sun tabbatar da hukuncin kafin a aiwatar dashi.

Lauyoyin da suka kare Hassan Adamu sun sha cewa yayi abun da yayi ne domin kokarin kare kansa daga Umar Aka sakamakon rigima da ta shiga tsakaninsu har ta kai ga shi Umar ya kama Hassan Adamu da kokawa..

Mai shari'an ya sake yanke wani hukunci na biyu ga wani sojan mai suna Ibechi Oze wanda ya bace daga wurin aiki har na watanni goma har rundunar sojin kasar ta bada sanarwar ya bace amma kuma yana nan a raye. Ya batarda sawu ne lokacin da aka turasu bakin daga a Gwozah.

Ibechi Oze yayi ikirarin cewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne suka saceshi kafin, wai ya samu ya kubuta lokacinda sojin sama suka kai hari kan 'yan Boko Haram din. Kotun ta yi watsi da cewa bindigarsa ta bace tare da wasu harsashai. Amma abun da ya tona masa asiri shi ne lokacin da aka ce ya bata yana zuwa yana karban albashinsa ba tare da zuwa aiki ba.

Daga karshe dai Birgediya Janar Olusegun Adeniyi ya yanke masa hukuncin watanni goma sha hudu a gidan kaso.

Sakataren kungiyar lauyoyin Maiduguri Barrister Mohammed Umar ya gamsu da hukuncin da aka yiwa Hassan Adamu.

A karshen jawabinsa mai shari'a Adeniyi yace matsayin dokar soja shi ne duk wanda aka yanke masa hukuncin da ya kaishi gidan kaso tamkar an koreshi ne daga aikin soja.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG