Acewar gwamnatin Zamfara kasa shawo kan matsalar ta hanyar yin anfani da karfin jami'an tsaro ya sa dole ta yanke shawarar bin tafarkin sulhu da sasantawa domin kawo karshen kai hare-hare a garuruwan jihar da kashe kashen rayukan jama'a da satar shanu da mutane domin neman kudin fansa da suka kwashe shekaru da dama suna addabar jihar.
Wani babban kwamitin sulhu da mataimakin gwamnan jihar ke yiwa jagoranci ya samu nasarar shawo kan 'yan bindigan Fulani da na 'yan sa kai inda a wani taro a fadar gwamnatin jihar dake Gusau suka kulla yarjejeniyar sasantawa da kuma mika makamansu ga gwamnati.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Wakala shugaban kwamitin sasantawa yayi karin bayan. Yace an kwao 'yansanda da sojoji amma duk basu kaiga cin nasara ba sai da Allah ya sa suka bi hanyar tattaunawa da mutanen. Suna bin kowace karamar hukuma da kowace masarauta suna tattaunawa da kowane bangare.
Bayan sun kare bin kananan hukumomin sai gwamnati ta shirya wa sarakuna da shugabannin Fulani da kungiyoyin sa kai su zo taron tattaunawa kai tsaye domin a tabbatar cewa yarjejeniyar da aka cimma akan zaman lafiya an yadda da ita kuma an tabbatar da ita.
A wajen taron shugabannin da dama suka yi jawabi. Bayan sun gabatar da korafe korafensu sun tabbatar da samar da zaman lafiya inda suka ce da yadda Allah ba zasu sake tayar da hankalin kowa ba.
To sai dai gwamnatin jihar tare da shugabannin hukumomin tsaro sun tabbatar da daukan kwararan matakai domin kawar da makamai daga hannun jama'a.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.