Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Karrama Dan Najeriya Mai Shekaru 14 Da Lambar Yabo


Kanyeyachukwu Tagbo Okeke
Kanyeyachukwu Tagbo Okeke

Magajin garin Newark, New Jersey a Amurka, Ras J. Baraka, ya karrama Kanyeyachukwu Tagbo Okekene a ranar Lahadi da lambar yabo, a yayin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya karo na 8 a jihar.

A cikin wata wasika da aka sanya wa hannu, magajin garin ya yaba wa Kanyeyachukwu saboda hidimarsa, aikin jagoranci, da kuma jajircewa wajen taimaka wa al'ummomi a kewayensu.

Kanyeyachukwu, wanda iyayensa 'yan garin Amichi da ke Jihar Anambra a Najeriya ne, an haife shi ne a garin Calgary da ke kasar Canada. Yana zane-zane, wanda fasaha da sana'arsa suka bambanta shi da takwarorinsa.

An haife Kanyeyachukwu Tagbo Okeke a watan Nuwamba na shekarar 2009, kuma matashi ne wanda zanen shi ya haskaka bangon gidajen tarihi da dama a Najeriya, Turai, da sauran sassan Afirka a cikin 'yan shekarun da suka gabata, inda ya samu karbuwa sosai.

A cikin shekarar 2019, an karrama shi a matsayin wanda ya karɓi lambar yabo ta ranar ‘yancin kai ta Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG