WASHINGTON, DC —
Al'ummar garin Duguri dake karamar hukumar Alkaleri cikin jihar Bauchi sun himmatu da shirin takalar cizon macizai da ya addabesu.
Kafin matakin da aka dauka yanzu garin Duguri ya yi asarar rayukan mutane da yawa sanadiyar cizon muggan macizai. Wasu ma da dama sun nakasa sabili da sarar da suka samu daga macizai. Masana sun ce ambaliyar ruwan sama da aka samu a daminar bara shi ne ya jawo yawan macizai a Dugurin.
A ganawarsu da manema labarai mai magana da yawun al'ummar Duguri ministan birnin tarayya wato Abuja, Sanato Bala Mohammed Kauran Bauchi ya yi bayani kan saran macizan. Ya fara da godewa kafofin labarai musamman na kasashen waje wadanda ya ce sun taimaka kwarai da gaske wajen tunatar da al'umma da kuma shugabanni dangane da irin annobar da ta faru a garin mahaifarsa Duguri. Sabili da ambaliyan ruwa da suka samu daga jihar Filato sun samu kububuwa masu kashe mutane. Yanzu haka a matsayinsu na 'ya'yan Duguri ya ce sun hada kudi sun sayo magunguna da zarar maciji ya sari mutum ya kasance an bayar da magani nan take. Kodayake yanzu macizan basa kashe mutum domin magunguna shi da gwamnatin Bauchi zasu hada karfi da karfe su gina asibiti musamman domin maganin maciji.
Sanato Bala Mohammed ya ce gwamnati bata gaza ba domin da ita gwamnatin jiha da ta tarayya suna masu hanyoyi da zaizayan ruwa. Abubuwan da su 'yan kasa da karamar hukuma zasu iya yi su taimaki kansu dole su yi.
Ga karin bayani.