Ya ce shi yana goyon bayan shugaba Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takara domin ya kara wa'adi na biyu na shekara hudu. A cewarsa wa'adin shekara hudu ba zai kashe 'yan arewa ba. Kuma tsayawar shugaba Jonathan ta zama alheri idan a ka yi la'akari da yadda a karkashin mulkinsa aka gyara wuta da hanyoyi da suka shiga arewa. Wasu wurare ma da ba hanyoyi kamar daga Gombe zuwa Bauchi yanzu an samesu wasu kuma ana kan ginasu. Sanato Bala ya ce saboda haka zaman Jonathan a matsayin shugaban kasa ba abu ba ne da ya zama annoba ba ga mutanen arewa. Mulkinsa ya zama wa arewa alheri kuma yana bin hanyar ka'idan inda aka sa arewa a siyasance. Ya ce babu abun da arewa bata da shi a gwamnatin shugaba Jonthan sai dai kujerar shugaban kasar.
Ministan ya cigaba da lissafa mukaman da 'yan arewa ke rike dasu a gwamnatin shugaba Jonathan kamar mataimakin shugaban kasa da shugabannin majalisun tarayyar kasar da gwamnan babban bankin Najeriya da wasu ma da yawa rike da manyan guraba.
Sanata ya ce abun da ya kamata 'yan arewa su yi shi ne su hada kai su taimaki alummar arewa ba wai canza manufa ba suna nuna yatsa ma juna. Da aka ce Jonathan baya taimakar arewa kuma an yi misali da taimakon nera biliyan biyu kacal da ya ba jihohi shida na arewa maso gabas alhali kuwa biliyan 12 ya baiwa jiharsa. Sanatan ya ce ai wannan alfarma ce ya yi masu domin basu nema ba. Shugaban ya je taronsu ne ya bada kudaden domin su fara aikin farfado da tattalin arzikin jihohinsu. Ya kara da cewa sanin kowa ne cewa kudaden da a ke kashewa kan harkokin tsaro a arewa maso gabas suna da dimbin yawa. Duk da haka gwamnatin tarayya ta bada shinkafa da abinci ma wuraren dake cikin matsalar tsaro. Kuma wai ana abubuwa na tsakanin da Allah da zasu kawo cigaba.
Gyara arewa maso gabas zai ci kudi da yawa kuma shugaban kasa a shirye yake ya bada duk kudin da ake bukata. Ya kamata irinsu su mara masa baya suna yawo kawunan mutane kan ayyukan da shugaba Jonathan ke yi. Ya ce yadda shugaban bai samu kashin 20 cikin dari ba a zaben 2011 bai yi masa dadi ba. Sai aka tambayi ministan cewa baya ganin lamarin ya nuna jama'ar Bauchi ta gaji da PDP da shugaba Jonathan? Sai ya ce ra'ayin mai tambayar ne amma ba ra'ayin mutanen Bauchi ba ne.
Ga karin bayani.