Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

McCain Tsohon Dan Takarar Shugaban Amurka Ya Rasu


John Sidney McCain
John Sidney McCain

Dan majalisar dattawa a Amurka John McCain ya rasu a jiya Asabar yana da shelaru 81, bayan fama da ya yi da cutar sankarar kwakwalwa, mutumin da aka kwatanta da dattijon Amurka, mai kishin kasarsa kuma gwarzo.

Matarsa Cindy ta rubuta a kan shafinta na Twitter tana cewa, tana cikin alhini, kuma ta yi nasarar kasancewa a cikin mutanen da shi dan kansa yake fadin masoyansa, a wurin da ya fi so.

Daya a cikin ‘ya’ya biyar na marigayin, Meghan, ita ma ta dora a kan shafinta na Twitter tana mai cewa, tana tare da mahaifinta a karshe, kamar yanda ta kasance da shi tun da farko.

An fi sanin marigayi ne da wanda ya tsira a cikin fursinonin yakin Vietnam kuma ya zo ya ya yi nasarar zama dan takarar jami’iyar Republican a zaben shugaban kasar Amurka a shekarar 2008. John Sidney McCain dai cikakken mai kishin Amurka ne.

Yace muna cikin kasa mai cike da walwala, kasar da komai ke yiwuwa, inji McCain a wani jawabi da ya yi a ciki watan Oktoba, a cibiyar kundin tsarin mulki ta kasa, watanni bayan an same shi da cutar sankara, inda aka ba shi lambar yabo ta Liberty. Yace Allah Ya albarkace mu, mu kuma muna kyautatawa mutane.

A cikin wannan jawabin, ya kuma yi kashedi a kan irin hadari dake tattare da zamanin mulkin shuagaba Donald Trump.

Bayan shekaru da dama, a matsayinsa na dan majalisar dattawan Amurka, McCain ya koma Vietnam inda ya yi kokarin karfafa alaka tsakanin Washington da Hanoi, inda ya fadawa Muryar Amurka cewa a manta baya kuma a jiri gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG