Wadanda suka tsira sun ce kamar mutane 450 zuwa dari shida cikin har da mata da kananan yara da dama aka cusa a cikin jirgin ruwar da ya nitse a garin Rosetta mai tashar jiragen ruwa, aka tasar wa nahiyar Turai.
Hukumomin sojin kasar Misra sunce galibin wadanda abin ya shafa duk ‘yan asalin kasar Masar ne daga yankin jihar Nile Delta kuma mafi yawansu matasa ne da suke kokarin ketarawa zuwa Turai don inganta rayuwarsu.
Amma kuma wasu rahotanni na cewar akwai ‘yan kasashen Afrika da dama da kuma wasu daga Syria a cikin jirgin.
Yan Sanda Masar sun fada a ranar Litinin an tsare mutumen da ya mallaki jirgin ruwan wanda zai iya huskantar shari’ar laifin yin simoga din mutane da da kuma kisan kai.
Hukumar yan gudun hijira ta duniya tace bakin haure dubu uku da dari biyar ne suka mutu ko kuma suka bata a wannan sheakara yayid da suke kokarin ketara teku Mediterranean.
Hukumar tace adadin ya nuna cewa mutanen da suka mutu a bana sunfi na bara da misalin mutane 600.