Duka 'yan takarar biyu na fuskantar kalubale mai girma. Ba game da abubuwan da 'yan takarar su ke fadi ne kawai 'yan kallon za su mai da hankali ba, har ma da yadda su ke maganar da kuma yadda su ke mai da martani ga juna.
Muhawarar za ta kasance wata muhimmiyar dama ga Trump, wanda ya cimma Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat a akasarin kuri'un jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan, musamman saboda ya nuna natsuwa fiye da yadda ya nuna a baya. Ya kuma mai da hankali kan sakonninsa.
A tana bangaren kuma, Clinton za ta iya amfani da muhawarar wajen sake bayar da kwarin gwiwa ga magoya bayanta, ta kuma kara jaddada alkawarinta na gina tattalin arziki mai alfanu ga kowa, kamar yadda ta yi a wani gangami na bayabayan nan a Orlando, jahar Florida.