Shugaban cibiyar yaki da cutar kuturta ta Nigeriya, Mr. Steven Okpanachi ne yayi wannan kiran a sokoto yayin kaddamar da wani shiri. Shugaban cibiyar yace gwamnatoci suna bukatar sake hada iyalai da aka raba saboda dokokin na da suka sa aka raba wadanda suke fama da cutar kuturta da ‘yan’uwansu. Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi su taimaki iyalan wadanda suka yi jinya ta wajen kyale su su ci gaba da zama a gidajen da aka gina domin jinyar masu fama da cutar kuturta idan basu so su koma su ci gaba da zama cikin sauran al’umma.
Yace idan kuma ya zama dole mutanen su sake matsugunansu dole ne a ba mutanen dammar taka kyakkyawar rawa a zabar wurinda zasu zauna a kuma inganta wuraren zamansu. Yace ya kamata gwamnati tayi wani tsarin da zai taimaka a dauki matakin rufe gidajen jinyar kutare baki daya a kuma taimaki wadanda suka dade suna jinya a wurin su sake sha’awar zama tare da iyalansu tsakanin al’umma.
Yace mutanen da suka kamu da kuturta da iyalansu suna da damar shiga cikin shawarwari da shirye shirye da suka shafi rayuwarsu. Shugaban yaki da cutar kuturta yace an shirya taron ne domin kara ilimantar da ma’aikatan da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da suke taimakawa wajen jinyar masu fama da cutar kuturta da kuma mutanen da suka kamu da cutar kuturta domin su san damar su.
Ya kuma nuna cewa an shirya shi ne domin taimakon mutane da ayyukan hannu domin su gane abinda ke kawo talauci da kuma illarsu, yayi kira ga al’ummar jihar su daina nunawa mutanen da suka kamu da cutar kuturta banbanci.