Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kyanda Ta Kashe Mutane 29 a Jihar Naija


Wani dan yaro yana karban rigakafin cutar kyanda
Wani dan yaro yana karban rigakafin cutar kyanda

Kimanin mutane 29 suka mutu ta dalilin kamuwa da cutar kyanda a jihar Naija

Kimanin mutane 29 suka mutu ta dalilin kamuwa da cutar kyanda a jihar Naija. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Ibrahim Sule ne ya bayyana haka a Minna fadar gwamnatin jihar a lokacin kaddamar da yaki da cutar ta wajen yin allurar rigakafi a garin Beji cikin karamar hukumar Bosso ta jihar.

Da yake bada bayanin wadanda aka yiwa maganin cutar a karamar hukumar, Dr. Sule yace, marasa lafiya 2,000 aka yi rajista a wannan shekara. Kwamishinan yace wannan shiri wani maida hankali ne na wannan gwamnatin domin kawar da cututtukan kananan yara masu kisa a jihar. Kwamishinan ya kuma dauki lokaci yana yiwa jama’a bayani a kan yadda cutar take yaduwa. Yace, cutar tana kamun yara ta hanyar kwayar cuta dake yawo a iska. Alamun cutar sun hada da zazzabi mai zafi, yoyon majina da jan idanu, kwanaki da yawa bayan nan, sai kuraje su fito daga fuska zuwa sauran jikin.

Cutar kyanda zata iya janyo cututtuka da yawa hadi da makanta, matsalar kwakwalwa, ciwon kunne, da ciwon nimoniya kuma babu wani cikakken magani na wannan cutar ta Kyanda. Yin allurar rigakafi ta cutar kyanda ta yara hadi da sauran allurai na rigakafi wasu manyan hanyoyi ne na kawar da barkewar wannan cutar.

Kwamishinan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Naija zata yi iyakacin kokarinta domin kauda wannan kalubalar da ake fuskanta da allurar rigakafin, da kawadda cututtuka, ta wurin kin yarda da rigakafin da wadansu iyaye suke yi.

Yace, za a yiwa yara tsakanin watanni 9 zuwa 59 allurar rigakafin wadannan cututtuka kuma ma’aikatan lafiya zasu bada wata takardar shaidar yin wannan allurar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG