An sako mutane uku a rukunin farko na wadanda ake Garkuwa da su a Gaza haka kuma rukunin Falasdinawa na farko da ake tsare da su a gidajen yari Isra’ila sun shaki iskar ‘yanci, a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da mayakan Hamas mai Rauni bayan shafe watanni 15 ana gwabza yaki cikin wan yanayi mai sosa rai, wanda matakan gaba da za a dauka cikin makonni 6 suke da wahala.
Falasdinawa a fadin Gaza sun kama hayar komawa gidajen su, sannan motar kayakin jinkai na farko y afara isa yankunan da aka daidaita.
Motocin safan da ke dauke da fursunonin sun fice shingen gidan yarin Isra’ila Ofer, dake wajen birnin Ramallah a yankin yammacin kogin Jordan, yayin da aka fara wasar wutar tartsati don nuna farin ciki.
Falasdinwa sun kewaye motocin na safa wasu kuma suka hau saman motocin sufa furta kalaman farin ciki.
Dandalin Mu Tattauna