Ma’aikatar bitalmalin Amurka ta fada a jiya Juma’a cewa ta dora hannu a kan kadarorin Nicolas ko kuma Nicolasito Maduro Jr. dake cikin Amurka kana ta haramtawa Amurkawa da kasuwancin Amurka yin huldar kasuwanci da shi.
Sakataren bitalmalin Amurka Steve Mnuchin ya fada a wata sanarwa cewa shugaban Venezuela yana dogara ne a kan Nicolasito da wasu abokansa na kud-da-kud a mulkinsa ne yake ci gaba da rike tattalin arzikin kasar da kuma gallazawa mutanen Venezuela.
Ma’aikatar bitalmalin ta kuma zargi Maduro Jr. da aikata farfaganda da hana 'yan kasar cin gajiyar ma’adinan Venezuela da kuma matsawa sojojin kasar su hana shiga da kayan taimako zuwa cikin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin na Venezuela ya tilastawa miliyoyin mutane barin gidajen su daga kasar tun cikin shekarar 2015.
Facebook Forum