Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neman Shiga Amurka Yasa Uba Da Diya Sun Mutu A Kogi


An tsinci gawar wani mutum da ‘yarsa da suka fito daga kasar El Salvador a ranar Litinin, bayan da suka yi yunkurin tsallaka rafin da ake kira Rio Grande River, daga Mexico zuwa cikin Amurka, yayin da suke kokarin danganawa da Amurka a matsayin bakin haure.

Wata jaridar kasar Mexico da ake kira La Jornada ce ta fara wallafa hoton gawarwakin, wanda ya karade kafafen yada labarai da na sada zumunta, lamarin da har ila yau, ya kara janyo hankulan jama’a kan irin tsawon lokacin da bakin haure ke kwashewa, suna jira kafin a tantance bukatarsu ta neman mafaka akan iyakoki.

A cewar jaridar ta La Jornada, da kuma kamfanin dillancin labarai na Associated Press, mahaifin yarinyar mai suna Oscar Alberto Martinez Ramirez, ya harzuka ne, saboda tsawon lokacin da ya kwashe yana jiran damar da zai mika takardunsa na neman mafaka a Amurka.

Hakan ya sa a daren ranar Lahadi, ya yanke shawarar tsallaka rafin tare da ‘yarsa.

Rahotanni sun ce, Ramirez ya yi nasarar tsallakawa da ‘yar tasa mai watanni 23, zuwa daya gabar ruwan, amma bayan da ya koma ya taho da matarsa, wato mahaifiyar yarinyar, sai ‘yar ta shiga cikin ruwan, inda shi kuma ya yi yunkurin ceto ta, amma sai igiyar ruwa mai karfi ta tafi da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG