Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Hukumar Yi wa Kamfanoni Rajista A Najeriya Ta CAC Sun Tarbi Sabon Shugabansu


Sabon shugaban CAC a Najeriya, Hussaini Ishaq Magaji (SAN)
Sabon shugaban CAC a Najeriya, Hussaini Ishaq Magaji (SAN)

Ma'aikatan hukumar yi wa kamfanoni rajista ta Najeriya "Corporate Affairs Commission" sun yi gangamin nuna farin cikin rashin sabuntawa shugaban hukumar Barista Garba Abubakar sabon wa'adi bayan shafe shekara uku da wata tara kan kujera.

ABUJA, NIGERIA - Ma'aikatan sun zayyana tsohon shugaban na su da wanda ya gurgunta hukumar da danne hakkin ma'aikata.

Lokacin Da Ma’aikatan Hukumar Yi Wa Kanfanoni Rejista A Najeriya CAC Suka Nada Sabon Shugaba
Lokacin Da Ma’aikatan Hukumar Yi Wa Kanfanoni Rejista A Najeriya CAC Suka Nada Sabon Shugaba

Tun sanar da nada sabon shugaban hukumar Hussaini Magaji da shugaba Tinubu ya yi a rukunin nade-nade da shugaban hukumomin ma'aikatar kasuwanci; ma'aikatan suka zuba ruwa a kasa suka sha don rabuwa da Barista A.G. Abubakar wanda jikan Firaminista, Sir Abubakar Tafawa Balewa ne.

Yadda ma'aikatan hukumar suka kafa wani kyalle mai dauke da nuna farin cikinsu da tafiyar A.G. Abubakar
Yadda ma'aikatan hukumar suka kafa wani kyalle mai dauke da nuna farin cikinsu da tafiyar A.G. Abubakar

Shugaban kungiyar ma'aikatan da suka yi shagali a gaban helkwatar hukumar a Abuja, Komred Dokta Ibrahim Kirfi, ya ce yanzu sun samu sabuwar fata ta ingancin aiki "Gaskiya AG. Abubakar bai dau halin marigayi Tafawa Balewa ba don ya dade yana danne hakkin ma'aikata.

Yanzu zamu hada kai da sabon shugaban hukumar don kawo nasarorin da za su taimaki tattalin arzikin Najeriya."

Ma’aikatan Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista A Najeriya ta
Ma’aikatan Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista A Najeriya ta

Shi ma ma'ajin kungiyar ma'aikatan, Komred Shamsuddeen Umar Dungus, ya ce tsohon shugaban ya sauya masa wajen aiki da manufar da ba ta dace ba.

Muryar Amurka ta tuntubi AG. Abubakar don jin martaninsa inda ya ce ba zai ce komai ba.

Amma ya yi amannar cewa yana da shaida mai kyau a duk inda ya yi aiki don haka a tuntubi jami'an labarun hukumar.

Wani ma'aikaci a hukumar ta CAC
Wani ma'aikaci a hukumar ta CAC

Rasheed Mahe jami'in labarun hukumar ne da ke cewa ba wani tasiri da gangamin ma'aikatan ya yi.

Hukumar yi wa kamfanonin rajista na daga manyan cibiyoyin da ke samawa gwamnatin Najeriya biliyoyin Naira don haka a ke daukar wanda a ka nada shugaban hukumar ya tafi ma'aikata mai tsoka.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Ma'aikatan Hukumar Yi wa Kamfanoni Rajista A Najeriya Ta CAC Sun Tarbi Sabon Shugabansu
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG