Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Layin Karbar Tallafi Da 'Yan Najeriya Ke Yi Ganiyar Rashin Sanin Kimar Kai Ne - Bishop Kuka


'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa Yayin Karbar Kayan Tallafi
'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa Yayin Karbar Kayan Tallafi

Malamin Addinin Kiristan nan na Najeriya Bishop Mathew Kuka ya caccaki tsarin yadda ake rabon kayan tallafi ga 'yan Najeriya a daidai lokacin da halin matsin rayuwa ke kara ta'azzara a kasar.

WASHINGTON DC - Sakin harkar musayar Naira ba tare da kaidi ba da janye tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya tayi ne suka sabbaba mummunar hauhawar farashin kayan masarufi data haifar da tsadar rayuwa.

Gwamnatoci a dukkanin matakai sun bijiro da matakan rabon tallafi ga tallakawa ciki harda rabon kayan abinci a kokarin rage radadin halin matsin da ake ciki a fadin Najeriya.

Saidai Kuka, wanda ya kasance Limamin Darikar Katolika mai kula da Shiyar Sokoto, yana ganin cewar hakan kaskanta dan adam ne kuma kamata yayi gwamnatoci su bullo da tsare-tsaren shawo kan matsalolin dake addabar Najeriya.

Malamin Addinin ya shaida a cikin shirin siyasar tashar talabijin ta Channels na ranar Lahadi "Sunday Politics" a turance cewar, "muna bukatar ganin tsare -tsaren da gwamnati ta bijiro dasu domin fiddamu daga wannan matsala ba wai muyi layin karbar tallafi tamkar muna halin yaki ba.

"Ina ganin ganiyar rashin sanin kimar dan adam ne 'yan najeriya suna layi kullum karkashin zafin rana domin karbar buhun shinkafa ba wai don ba'a bada kudi ba, a'a sai kawai kawo ya san yadda kudaden ke zurarewa kafin su kai ga jama'a. ba sadaka 'yan najeriya ke bukata ba."

Ya kuma baiwa gwamnatin tarayya shawara akan shawo kan rashin tsaro domin magance matsalar baki daya.

Bishop Kuka ya jaddada cewar, "burin manomanmu shine komawa gonakinsu, mutane na son kamawa kan rayuwar da suka saba da ita magance matsalar tsaro shine matakin farko na magance matsalar. Samarda tsare-tsaren magance matsalar tsaro shine matakin kawo karshen matsalar."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG