Wani sabon sauro dauke da wata kwayar cuta na kara jan hankalin kasashen duniya yanzu haka saboda illar da ya ke haifarwa da ta shafi kwakwalwa, laka, da jijiyoyin da suka hada su da kuma yadda kwayar cutar ke bazuwa da sauri.
Kwayar cutar mai suna Zika, wani nau’in sauro ne da ake kira aggressive Aedes aegypti a turance ke dauke da ita, yanzu haka dai ta bazu a akalla kasashe 23.
Cibiyar kula da magance cututtuka ta Amurka ta gargadi mata masu juna biyu akan cewa kada su je wadannan kasashen haka kuma jami’an kiwon lafiya a yawancin wadannna kasashen na shawartar mata akan kada su dauki juna biyu, har nan da shekaru biyu masu zuwa.
Kwararru sun fadi cewa wannan wata annoba ce da ke bazuwa a hankali, ba kuma mutuwa ta ke da kanta ba, sai dai ma muni da take yi sannu a hankali.