Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Barazanar Tsaro Ga Ziyarar Da Kwankwaso Zai Kai Kano – ‘Yan Sanda


Taron Manema Labarai Na Kungiyar Kwankwasiyya
Taron Manema Labarai Na Kungiyar Kwankwasiyya

Hukumar ‘yan sanda a jihar Kano tace tana kan bakanta cewa, akwai barazanar tsaro ga ziyarar da tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso ya shirya kaiwa a gobe Talata.

A juma’ar data gabata ne, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Rabiu Yusuf ya sanar da manema labarai cewa, bayanan sirri da rundunar ta samu na nuni da cewa, wasu tsageru na yunkuri tada fitina a yayin ziyarar da sanata kwankwaso yace zai kai Kano, hakan ya sa ta shawarci tsohon gwamnan ya dage ziyarar zuwa lokacin da lamura zasu dai-daita.

Sai dai sanatan wanda ya shafe fiye da shekara guda bai je Kano ba, yace ziyarar sa na nan Daram, kamar yadda magoya bayan sa karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin Kano Eng Rabiu Sulaiman Bichi suka shaidawa manema labarai a karshen mako.

Hakan dai na nuni da cewa, magoya bayan sanata zasu ci gaba da tarbar sa. Sai dai taron nasu ya zo dai-dai da gangamin da ita-ma Jam’iyyar APC reshen Kano kuma a wuri guda a can hanyar Kano zuwa Zariya.

To ko ita jam’iyyar APC zata janye nata zuwa wani lokaci tunda sanata Rabiu Kwankwason ya yi watsi da shawarar hukumar ‘yan sanda? Tambayar Kenan da wakilin Muryar Amurka ya yiwa sakataren Jam’iyyar Alhaji Ibrahim Zakari Sarina.

Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari domin jin amsar Zakari Sarina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG