Hukumar kwallon kafa ta kasar Somalia ta bayyana cewa tana shirin daukar dawainiyar wasan kwallon kafa na kasa da kasa a cikin shekara mai kamawa domin a samu ci gaba a harkokin tsaron kasar.
Shugaban hukumar kwallon kafa na kasar ne Abdqiani Said Arab yace lokaci yayi da kasar ta Somalia zata shirya wasanni kwallon kafa a babban filin wasan dake cikin kasar a shekara mai kamawa.
A cikin sanarwa dake dauke da sa hannun sa yace samun ingaci a harkokin tsaro a kasar, yasa suka yanke shawarar gudanar da wasannin cikin gida.
Yace mutanen kasar ta Somalia suna da damar kallon babban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar suna wasa a cikin gida, don haka yanzu lokaci yayi da zasu gudanar da hakan musammam ma ganin yadda kasar ke kara samun ci gaba.
Facebook Forum