A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyi sun kudiri aniyar fito na fito da mahukuntan kasar, bayan da su ka ce sun gano alamun ana yin watsi da bukatun magoya bayansu. Laifin da suka dora a wuyan Ministan kwadago, wanda su ke zargi da fifita wasu kungiyoyin ma’aikata akan wasu.
Ma’aikata a karkashin inuwar wasu kungiyoyin kwadago ke nuna alamar gajiya da halin ko in kulan da suka ce gwamnatin Nijar na nuna wa matsalolin ma’aikatan kasar. Sun bayyana haka ne a sanarwa da sakataren hadediyar kungiyar kwadago ta CSTN Yaou Mahamadou ya karanta.
Zaben da aka gudanar a watannin baya domin tantance kungiyoyin kwadagon da suka cancanci su wakilci ma’aikatan kwadago a gaban hukuma wani abu ne da USTN da kawayenta ke dauka a matsayin wata hanyar da gwamnati ke amfani da ita don fifita wasu kungiyoyi akan wasu. Amma Ministan kwadago Ben Omar Mohamed ya musanta wannan zargi.
Kungiyoyin da su ka fitar da wannan sanarwa a karksahin jagorancin kungiyar USTN sun lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya har sai sun ci nasara game da matsalolin da suka addabi ma’aikatan kwadago.
Ga rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum