Cikin kungiyoyi dake karkashin ta harda NUPENG, masu dakon man fetur, da ma'aikatan wutar lantarki da bankuna da kuma matuka jiragen sama da na kasa da dai sauranasu.
Sakataren tsare tsare na kungiyar Komared Nasir Kabir, wanda ya bayyana haka a wata hira da yayi da Muryar Amurka, ya ce kadan daga cikin matsalolin su harda Ministar Kwadago Dr. Ngige, wanda yace yana nuna son zuciya, ta wajen fifita kungiyar NLC, domin ya ki ya saki lasisin rijistar kungiyar ta ULC, da kuma rashin biyan ma'aikata albashinsu da gwamnonin jihohi suke yi.
Da yake sharhi kan illar yajin aikin ga tattalin arziki, shugaban sashen koyon ilmin tattalin arziki da dabarun kasuwanci a kwalejin kimiyya da Fasaha ta jahar Kano, Dr. Lawal Habeeb Yahya, yace hakan zai sake maida hanun agogo baya, ga tattalin arzikin da yake kokarin tsamo kan shi daga koma bayan da ya shiga, shekaru biyu da suka wuce.
Duk kokarin da Muryar Amurka ta yi domin jin matsayar ma'aikatar kwadago abin ya ci tura.
Domin karin Saurari cikakken rahotan Sahabo Imam Aliyu.
Facebook Forum