A dai dai lokacin da wakilan kwamitin majalisar ke sauraron bahasi daga mawallafin jaridar da ta buga wannan labari na zargin karbar na goro a kan gwamnan Kano, ayarin daliban makarantun Pramare ne suka mamaye gefen titin shiga majalisar dauke da kwaleye masu rubutun nuna goyon bayan ga gwamnan.
Ala’amarin dai ya sha caccaka daga bangarori da dama, musamman kungiyoyin rajin kare hakkin yara.
Kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa mai lakabin FIDA na cikin dinbin kungiyoyi da dubban mutane dake Allah wadai da wannan mataki.
Barr Amina Umar Hussain kenan sakatariyar yada labaru a reshen jihar Kano na kungiyar ta FIDA, tace tuni dai hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano da makaratun Pramare ke karkashin kulawar ta, ta mayar da martani dangane da wannan batu.
Shima Alhaji Ibrahim Zakari Bagwai shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano, yace hukamar bata da hannu a wannan abu kana bata goyi bayan wannan abu ba kuma ya tabbatar da cewa hukumar SUBEB zata gudanar da bincike domin hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki.
Yanzu haka dai kungiyar lauyoyin mata tace zata bibiyi aikin bincikar wannan batu da hukumar ta SUBEB tace zata yi, inji Barrister Amina Umar ke fadi.
Daga jihar Kano ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum