Babban madugun hamayya na kasar Saliyo ya yi kira jiya Laraba da a kwantar da hankali, a bayan da magoya bayansa suka bazu a kan tituna suna fito na fito da ‘yansanda, da yayi sanadin raunata akalla mutum guda bayan an wuni ana gudanar da zabe lami lafiya.
Julius Maada Bio ya shaidawa manema labarai a shelkwatar jam’iyar Sierra Leone Peoples party dake unguwar ‘yan gata ta Goderich a birnin Freetown cewa, "muna so jama’a su kwantar da hankulansu, su zauna lafiya domin mu samu ganin yin zabe cikin kwanciyar hankali a rayuwarmu."
An gudanar da zabe a kasar Saliyo jiya a wani abinda masu sharhi kan lamura suka ce yafi kowanne zafi a tarihin kasar. Bio yana kalubalantar Samura kamara na jam’iyar All People’s Congress mai mulkin kasar yanzu, da wadansu ‘yan takara goma sha hudu a zaben shugaban kasa. Shugaban kasa mai ci yanzu, Ernest Bai Koromah na jam’iyar APC zai sauka daga karagar mulki bayan kammala wa’adin mulki biyu.
An gudanar da zabe lami lafiya a duk fadin kasar, amma bayan rufe runfunan zabe, sai aka fara tashin hankali a Goderich bayan samun rahoton wata hatsaniya da ta auku a kofar shelkwatar SLPP inda kusoshin jam’iyar suka ce suna tantance sakamakon da ake fitarwa.
Facebook Forum