Taron na wannan shekarar ya fi maida hankali ne a kan rayuwar mata. Wadannan ko sun hada da ilimantar da su da kula da lafiyarsu. Alhaji Mohammed Umar Jabbi sarkin yakin Gaji shi ya wakilci Sarkin Musulmi, Mai Martaba Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III wanda kuma shi ne uban kungiyar na kasa gaba daya, a wurin taron.
Sarkin Musulmi yace aikin kungiyoyin ya fi na bada agaji kadai. Yace ana wayar da kawunan mata kan duk abun da zai taimaki rayuwarsu kamar kiwon lafiya da sha'ani tsafta da kiyaye muhalli da sha'anin tarbiya mai kyau da jin tausayi da hadin kai. Yace duk abun da maza keyi mata ma suna iya yi. Yace ilimin da Allah ya bamu na zamani yakamata a ilimantar da mata kansu domin su ilimantar da mata 'yanuwansu. Idan sun dauki ciki yakamata su san yadda zasu je awon ciki. Idan kuma gudawa ya zo su san abun da zasu yi. Yakamata kuma a koyawa mata addini yadda ake sallah da dai sauransu.
Taron ya tabo matsalar mutuwar mata musamman idan sun zo haihuwa da kuma mutuwar kananan yara. Da take mayarda martani shugabar mata ta kasa Hajiya Aisha Aliko Mohammed tace jihohin arewa su ne suka fi yawan mata dake mutuwa lokacin haihuwa. Yawancin matan dake mutuwa kuma matan karkara ne. Da yawa cikin matan dake mutuwa Musulmi ne tace kungiyarsu kuma ta Musulmai ne domin haka ya kamata su wayarwa matansu kai. Kidigdiga ya nuna cewa kusan mata dari ke mutuwa kowace rana idan sun zo haihuwa.
Hajiya Aisha tace wajibi ne su taimaki mata su gane mahimmancin zuwa asibiti. Lokaci ya yi da zasu tunkari gwamnati su ce sun shirya domin haka a tsare-tsarensu na horas da ungozomomi su kara kaimi domin su taimaki mata.
Mahalarta taron sun fadi albarkacin bakinsu. Wata Hajiya Rakiya Mukaila Ahmed daga jihar Imo tace sun karu da abubuwan da aka koya masu a wurin taron musamman ga su iyaye. Ita ma Maimuna Umar daga Damaturu jihar Yobe tace ta karu da abubuwa da dama. Tace an ilimantar dasu kan ilimin kimiya da yadda zasu bi da yara da matan aure har ma da maza musamman mutane karkara kan alamura da suka shafi rayuwa.
Masana da dama suka gabatar da kasidu da lakcoci.
Ga rahoto.