Kungiyar kwallon kafa ta Juventus, ta yi waje rod da Barcelona, a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL)2016/2017 sakamakon canjaras 0-0 da suka yi a jiya a karawarsu ta biyu inda akarawar farko Juventus, ta doke Barcelona, da ci 3-0.
A daya wasan da aka buga tsakanin Leicester City, da Atletico Madrid, antashi kunnen doki 1-1 wannan ya bada dama wa kungiyar Kwallon kafa ta Atletico Madrid zuwa zagaye na gaba Semi Final domin Atletico ta doke Leicester a karawarsu ta farko da kwallo 1-0
A yanzu haka dai kungiyoyi hudu ne suka Samu damar hayewa zuwa matakin wasan kusa da na karshe (Semi Final) kungiyoyin sune Real Madrid, Atletico Madrid, sai Juventus, da kuma Monaco.
Anasa ran gobe Jumma'a 21/4/2017 za'a fitar da jaddawalin kungiyoyin da zasu fafata a tsakaninsu don samun wanda zasu buga wasan karshe.
A yau ne kuma za'a dawo ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin Turai, Europa League 2016/2017 a matakin wasan kusa da nakusa da na karshe Quarter Final karawa ta biyu.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, zata kara da Anderlecht, sai Genk da Celta Vigo, Besiktas zata karbi bakuncin Lyon ne
Schalke 04 da Ajex.
Za'a buga wasannin da misalin karfe takwas da minti biyar na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi.