Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abun Kunya Ko Sha'awa! Uwa Ta Kwace Ma 'Yar-Cikin Ta Saurayi?


Uwa da ya
Uwa da ya

Abun kunya da yawa yake, amma wasu basu ganin shi a matsayin abun kunya. Babu wata kabila ko al’ada da zata iya karbar wannan abun a matsayin dai-dai, domin kuwa ya saba ma hankali. Marie Summers, mai shekaru 44, ta kwace ma ‘yar cikinta saurayi.

A cikin ‘yan kwanaki da suka gabata ne Marie da Anthony Key, tsohon saurayin ‘yarta suka saka zoben alkawalin aure. Duk da cewar mahaifiyar Danni, tasan wannan saurayin ne ta sanadiyar ‘yar-ta. Amma tace gaskiya tana son shi, wanda suka fara soyayya a tsakanin su, kuma ya yarda ya bar yarinyar ya dauki uwar a matsayin matar shi, nan dai da wasu watanni za’a daura auren su. Yarinyar dai ta bayyanar da cewar bazata halarci auren ba.

A lokacin da ake tanbayar yarinyar sai tace “Gaskiya bata taba tsanmanin mahaifiyar ta zata iya saka ta cikin damuwa ba, domin kuwa ta dauka uwa uwace. Amma sai gashi mahaifiya ta, ta zabi ta auri saurayi na. Bazan damu ba na hakura, amma bazan taba mantawa da irin cin amanar dake tsakani na da mahaifiya ta ba. Haka kuma ya bayyana mun cewar lallai jinni yafi ruwa kauri”

To wai idan kai ko kece ya za kuyi? Kurubuto muna ta shafin mu na www.facebook.com/voahausa

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG