Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tsofaffin Yan Sanda Sun Koka Kan Kudin Fansho


'Yan Sanda a Jihar Rivers, Maris 30, 2015.
'Yan Sanda a Jihar Rivers, Maris 30, 2015.

Kungiyar tsofaffin jami’an ‘yan sanda sun bukaci shugaban kasa da ‘yan Majalisar Tarayya da su duba batun yadda hukumar fansho ta ‘yan sanda ke biyan jami’an don yin gyara.

Shugabannin kungiyar wadanda suka fito daga sassa daban daban na Najeriya sun gudanar da babban taron su ne a birnin Jos, inda sukayi kukan cewa hukumar PENCOM tana zaluntarsu matuka wajen biyansu kudaden fansho.

Sakataren kungiyar tsafaffin ‘yan sanda na ‘kasa, yace sun kira wannan taro ne don fadakar da duniya halin da ake ciki, suna kuma kira shugaban Najeriya da ‘yan Majalisun Tarayya da dubi lambarin.

Shugabannin kungiyar tsofaffin ‘yan sanda sun kokawa hukumomi kan su taimaka musu a duba batun zaluncin da ake musu wajen biyansu kudaden fansho.

Saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG