Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Ruwa Dauke Da Bakin Haure 234 Ya Isa Malta


Jirgin ruwa mai suna "MV Lifeline" mallakar wata kungiyar bada agaji ta kasar Jamus ya isa Malta da bakin haure 234
Jirgin ruwa mai suna "MV Lifeline" mallakar wata kungiyar bada agaji ta kasar Jamus ya isa Malta da bakin haure 234

Bayan an kwashe mako guda ana kai komo akan bakin haure 234 kasashe takwas da suka hada da Malta sun amince su raba bakin hauren tsakaninsu

Bayan mako guda da aka kwashe ana arangama, wani jirgin ruwan agaji dauke da bakin haure 234 ya isa gabar tekun kasar Malta a jiya Laraba, yayin da wasu kasashen tarayyar turai su bakwai, suka amince su raba ‘yan gudun hijrar tare da Maltan, wacce kankanuwar kasa ce da ke kan tsibiri.

Kasar ta Malta, hade da Italiya da Ireland da Faransa da Luxembourg da Belgium da Netherland da kuma Portugal, sun cimma matsayar cewa za su raba ‘yan gudun hijrar a tsakaninsu.

Jirgin ruwan ya ceto bakin hauren ne a can gabar tekun Libya a ranar Alhamis din da ta gabata, kafin daga baya jirgin ya yi ta galantoyi akan tekun Meditareniya a ranar Juma’a, yayin da ake ta shawara kan makomar ‘ya gudun hijrar.

Wata kungiyar ba da agaji ta kasar Jamus ce ke da mallakin wannan jirgin ruwan wanda ake wa lakabi da Lifeline, wanda gabanin matsayar da aka cimma ta baya-bayan nan, Italiya ta ki amincewa jirgin ya tsaya a gabar tekunta, inda har Ministan cikin gidan kasar Matteo Salvini, wanda dan jam’iyar masu tsattsauran ra’ayin mazan jiya ne, ya ce ba za a mayar musu da kasa “sansanin ‘yan gudun hijra ba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG