Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Shiya tana zargin ana cigaba da yi mata bita da kuli


Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky, shugaban kungiyar Shiya ta Najeriya
Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky, shugaban kungiyar Shiya ta Najeriya

Kungiyar shiya ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da kakkausan lafazi tana kokawa akan abun da ta kira cigaba da yi mata bita da kuli wajen rushe gine-ginensu da kuma tono kabarurukan 'yan uwansu tun da kungiyar ta yi artabu da sojoji.

Koke-koken kungiyar na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Najeriya suka ce zasu gudanar da cikakken bincike akan aukuwar lamarin da kuma yin alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Akan wannan batun ne Muryar Amurka ta tuntubi Malam Yakubu Yahaya daya daga cikin na hannun daman Malam Ibrahim El-Zakzaky shugaban kungiyar shiya domin samun karin haske akan koke-kokesnu.

Malam Yakubu yace bayan duk abun da sojoji suka yi masu wai sai suka sake komawa suka rusa abun da ya saura. Banda haka sun je makabarta suka hako 'ya'yan El-Zakzaky amma kuma sai suka mayar dasu suka rufe.

Da Muryar Amurka ta jawo hankalin Malam Yakubu akan abun da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya fada akan husainiyarsu cewa ba'a ginata akan kaida ba sai Malam Yakubu yace idan an rusa husainiya ita kuma makabarta fa? Yace an kuma rusa gidan malamin nasu wanda cikin unguwa yake, ko menen dalilin gwamnati na yin hakan?

A jawabin da gwamnan jihar Kaduna ya yiwa jama'a ta kafar talibjan yace cibiyar husainiya wadda ita ce hedkwatar El-Zakzaky a Zaria sun ginata ne haka kawai ba tare da izini ba. Yace babu takardar mallakar fili duk da cewa a shekarar 2010 hukumar kula da gidaje da filaye ta jihar Kaduna ta rubuta sanarwar dakatar da aikin ginin. Daga baya har ta rubuta takardar rushe ginin. Basu dakatar da ginin ba su kuma mahukuntan Kaduna na wancan lokacin sai suka kawar da idanunsu daga ginin. Saboda haka sun sabawa dokar jihar.

Gwamnan ya cigaba da cewa gina husaniyar ta kuntatawa jama'a da dama musamman ganin cewa akan bababr hanya aka ginata..

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG