A wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Kaduna, matamakin shugaban kungiyar na kasa Malam Usman Yusuf Dutse ya ce ba zasu dakatar da yajin aikin ba sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da ta yiwa kungiyar. Ya ce gwamnatin tarayya ta nuna halin ko inkula game da ilimin kimiya da fsaha a Najeriya. Yajin aikin da suke yi kokari ne na kawo gyara wanda baya yiwuwa sai an ji jiki. Domin haka yana kiran iyaye su yi hakuri haka ma suma daliban su yi hakuri. Idan sun dawo za'a ga canji da yaddar Allah.
Suna da bukatu a gaban gwamnati da yawa. Sun kai wajen goma sha uku. Akwai yarjejeniyar da suka yi da gwamnati tun 2009 kuma a cikinsu babu wanda gwamnati ta cika. Kullum sai su bada hakuri har aka zo 2013 suka kuma bada hakuri da alkawarin cewa su zabi guda hudu da suka ce zasu yi.Sun yi alkawarin cika hudun cikin sati biyu amma basu yi ba. An basu wata daya, biyu har shekara basu yi ba. Dalili ke nan kungiyar ta koma yajin aiki.
Idan zasu cika hudun malaman zasu koma bakin aiki.To saidai bisa ga la'akari da yadda gwamnatin yanzu ke aiki bata damu da ilimi ba. Cikin kasashe 30 na Afirka da UNESCO ta bincikesu kan harkokin ilimi Najeriya ita ce ta zo karshe. Kananan kasashe kamar su Liberia da Togo da makamantansu sun fi Najeriya. A kasafin kudi yayin da wasu kasashe ke bada kashi 30 ga harkokin ilimi, Najeriya kashi 8 take bayarwa. Lokacin gwamnatin Abacha ne kadai aka taba bada kashi goma sha daya.
Abun da ya kama daga dakunan karatu da na kwana da kayan aiki irin wadanda an ma daina anfani da su duk sun lalace sun shude. Babu yadda za'a cigaba da tafiya haka. Dole a kawo canji.
Ga karin bayani.