Ita ma gwamnatin Gombe ta yi alkawarin taimakawa matar gwamnan da kokarinta na inganta rayuwar mata. Gwamnan jihar ne ya fadi hakan yayin bikin yaye shirin horas da mata kashi na bakwai. Ya ce ya ga yadda shirin ya baiwa mutane dubu hudu aiki kai tsaye. Idan kuma an yi la'akari da wadanda zasu ci gajiyar dubu hudun ana iya cewa mutane fiye da dubu goma sha shida suka samu abun yi. Ya ce suna goyon baya kuma zasu yi duk abun da ya cancanta dpmin a cigaba.
Matar gwamnan ta kira mata su kula da tarbiyar yara da mazajensu. Su tabbatar yara sun je makaranta domin rashin karatun ne ya cuci wasu. Ta ce dan taimakon da aka samu a zauna gida kada a soma gantali a gari ana yin batanci.
Malam Hassan Adamu mai baiwa matar gwamnan shawara kan ayyuka na musamman ya roki mata da basa cikin talauci su dena kutsa kai wurin neman dole sai an raba kayan taimakon da su. Wadanda suka fi karfin dubu hamsin bai kamata su mayar da kansu baya ba. Su bari a taimaki wadanda basu da karfi.
Ga karin bayani.