Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mata Gwauraye da Aka Cuta Sun Nemi Hkinsu


EFCC
EFCC

Shirin tallafawa mata gwauraye kuma iyayen marayu ya gamu da magudi

A cikin shekarar da ta gabata hukumar MDG ta zabi mata gwauraye kuma iyayen marayu guda 450 a kowace daya daga cikin kananan hukumomi hudu dake jihar Kano da nufin ba kowace tallafin nera 100,000.

Tallafin domin ya karfafa tattalin arzikin matan ne ta yadda ba zasu cigaba da dogaro ga kowa ba. Da tallafin zasu kafa tasu sana'o'in su ciyar da kansu da 'ya'yansu kamar yadda yakamata..

Ofishin mai baiwa tsohon gwamnan Kano shawara akan kungiyoyi da hukumomin bada tallafi ne ya kula da harkokin bada tallafin ga matan.

Amma sabanin kudin da MDG ta kayyade a baiwa kowace mace ba haka ya faru ba. Malama Kaltune da Hajiya Hauwa na cikin matan dake bayyana korafi game da lamarin.

Kaltune tace marayunta shida ne. An bata takarda da ta cike kana aka kirata a banki inda ta karbi kudi nera 100,000. To saidai da karbar kudin sai wasu jami'an gwamnati suka karbe suka zare nera 25,000 suka mayar mata da nera 75,000 akan cewa umurni aka basu daga sama.

Ita ma Hajiya Hauwa tace shugaban karamar hukumar Tarauni ya fada masu za'a basu kowannensu nera 100,000. Amma daga baya sai jami'an gwamnati suka zagaya suka karbi nera 25,000 daga kowace mace da sunan wai wahalolin da suka sha kudin su fito..

Kawo yanzu dai an gabatar da maganar ga hukumar EFCC domin ta bi digdigi. Barrister Audu Bulama Bukatti shi ne lauyan da ya rubuta wasikar koken.

EFCC zata binciki maganar su dauki matakin da yakmata.

Ga rahotn Ibrahim Mahmud Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG