Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar JIBWIS Ta Kafa Kwamiti Don Taimakawa Aikin Gona


Taron Kaddamar Da Kwamitin Noma Na Kungiyar JIBWIS
Taron Kaddamar Da Kwamitin Noma Na Kungiyar JIBWIS

Kungiyar JIBWIS ta Ahlus Sunna a Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin Noma don taimakawa matasa wajen dogaro da kai.

A wani abu mai dake nuna ‘kara sauya hanyoyin samun kudin gudanarwa a tsakanin kungiyoyin addini a Najeriya, kungiyar JIBWIS ta sanar da komawa gona daga damunar banan nan.

Kungiyar wadda kan samu tallafi daga taimakon mutane musamman ma a masallatai inda tun farko ta kirkiro wani shirin tallafawa marayu da miskinai ta hanyar sayan katin waya da aka tura daga Naira 100 mai suna Manara, a halin yanzu ta kaddamar da kwamitin Noma don dogaro da kai.

Kwamishinan kudi na jihar Gombe dake Arewa maso gabashin kasar Alhaji Hassan Mohammed, shine shugaban kwamitin, wanda ya ce za a inganta amfanin gona ta yadda za a ke fitar da su waje, ba wai kawai amfani da su a cikin gida ba.

Alhaji Hassan ya ce za a nemi ‘karin filayen Noma akan wadanda ake da su a yanzu, ya kuma tabbatar da cewa za a inganta noman ta yadda zai bayar da sha’awa.

Kungiyar JIBWIS za ta nemi filaye a kowacce jiha domin mutanen da suke da sha’awar aikin gona musamman matasa marasa aikin yi.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG