Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Operation Lafiya Dole Ta Kama ‘Yan Boko Haram 126


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Rundunar sojan Najeriya ta Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri, ta ce ta kame wasu mutane 126 da suke zargin cewa ‘yan kungiyar Boko Haram ne, wanda kuma ake zargi da kai hari garin Sabon Gari dake kan hanyar Biu.

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Majo Janal Lucky Irabor, shine ya shaidawa manema labarai hakan lokacin da yake jawabin ban kwana ga manema labarai a garin Maiduguri.

Irabor, ya ce idan ana iya tunawa kimanin makonni biyu da suka gabata wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari garin Sabon Gari, inda suka hallaka wasu jami’an soja shida tare da yiwa wasu raunuka, har ma da kwashe wasu makamai wanda yanzu haka an samu nasarar kwato wasu makaman.

Ya ci gaba da cewa suna samun bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram din da suka kai hari Sabon Gari na shirin kai hari garin Dambua, inda wasu daga cikinsu suka shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Dambua suka saje da mutane. Amma rundunar soja ta samu nasara a kansu.

‘Daya daga cikin mutanen da aka mutanen da aka kama an same shi da jakar ajiye kudi da ake kira wallet ta ‘daya daga cikin sojojin da aka kashen, tare da katin shaidar sojan da katin zarar kudi dukkanninsu mallamar sojan tare da mutumin da aka kame.

Janar Irabor, ya ce ko cikin kwanaki biyun da suka gabata an sami matsalar tashin bama bamai a garin Kwandiga, inda wasu ‘yan kunar bakin wake uku suka shiga suka tayar da bama-baman da ke jikinsu suka hallaka mutum guda.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG