Fursinoni saba'in da biyar sun tsere daga gidan yarin dake Akure babban birnin Jihar Ondo bayan da wasu dauke da makamai suka fasa gidan yarin jiya Lahadi.
Shugaban gidan yarin Jihar Ondo Mr. Tunde Olayiwola ya tabbatarwa manema labarai batun harin. Ya ce kawo yanzu ba zasu iya sanin ko su wanene suka kawo harin ba sai dai suna bincike. Ya kara da cewa wasu jami'an gidan yarin sun ji rauni sakamakon gumurzun da suka yi da maharan.
Wasu da abun ya faru a idanunsu sun ce maharan da suka yi na kare sun kai mutane dari da saba'in da biyar.
Maharan sun yi anfani da wani abu mai fashewa da ya tarwatsa kofar shiga gidan yarin wadda take da tsaro. Cikin wadanda suka tsere har da wadanda suka aikata manyan laifuka aka kuma yanke masu hukunce-hukunce masu tsanani.
Hassan Umar Tambuwal nada karin bayani