Al’umah ku tashi ku kama sana’a, dogaro da kai shine babban ginshikin rayuwa. Malama Hafsat Dan-maisoro, wata mace mai bautar kasa da take amfani da hanyoyin yanar gizon don tallata hajar ta ga masu bukata.
Ta fara wannan sana’ar tun kimanin shekara daya da suka gabata, kuma yanzu haka tana bautar kasa wanda bata dogara da wannan aikin kawai ba, ta kan sari kaya takai inda take aikin ta don tallatama ma’aikata, kuma a lokutta da dama ta kan dauki hoton hajarta, ta sa a shafinta na Instagram, facebook, da dai sauran hanyoyin sadarwa, wanda ta haka kuma tana samun alkhairi mutane nasiyan kayanta a ko ina.
Babban kiranta ga matasa shine su tashi tsaye wajen tallafawa kansu da kuma dogaro, sannan kuma su sani wannan hanyar yanar gizon tanada matukar mahimanci ga matasa wajen neman zama wani abu batare da anyi amfani da wannan kafar kawai ta zumunci ba kokuma ace matasa na amfani da wannan damar wajen bata suna.