Khalil ya ce yin haka zai tamaka gaya, wajen shawo kan rikicin da ke faruwa tsakanin Makiyay da Manoma, da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar.
Sai dai Kwararru na ganin yin hakan zai yi wu, amma Fulanin sun hada kawunansu wuri daya.
A lokacin da ya ke zantawa da Manema labarai bayan wani taro da suka yi a Abuja, shugaban Kungiyar, Mohammed Bello Khalil ya ce Kungiyoyin suna ganin kafa wannan ma'aikata zai taimaka wajen dakile ayyukan ta'addanci, da rashin jituwa da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakanin manoma da makiyaya.
Khalil ya ce ba wani abu mai yawa Makiyaya suke nema ba, su dai su samu inda za su ba dabbobinsu abinci mai kyau da kuma ruwan sha mai kyau.
A cewrsa, ba za su yi yawon neman abinci ba balle har su shiga gonan wani manomi har ya zama masu abin tashin hankali.
Sai dai wani bafillatani kuma mai nazari a al'amuran yau da kullum Janar Garus Gololo mai murabus ya ce lallai wannan kira ya yi masa dadi amma akwai wani abin dubawa a lamarin.
Gololo ya ce Gwamnati za ta iya daukan Matakin Kafa Ma'aikatar Makiyaya amma fa sai dai in Fulani makiyaya sun hada kansu.
Ya kara da cewa, Kungiyoyi Fulani Makiyaya sun yi yawa a kasar, kuma ba don komi ba sai don neman shugabanci.
Shi kuwa Sanata Mai wakiltan Jihar Borno ta Kudu Mohammed Ali Ndume ya ce a baya an yi irin wannan Ma'aikatar saboda haka shi zai goyi bayan wannan bukata idan an kawo ta Majalisar Dattawa.
Ndume ya ce wannan yunkuri ne mai kyau, kuma yana ganin zai taimaka sosai wajen kawar da rikice rikicen da ke ta faruwa tsakanin Manoma da Makiyaya. Ndume ya ce tabarbarewar da ake fuskanta a fanin tsaro zai ragu sosai.
Kungiyoyi irin su Miyetti Allah Kautal Hore da MACBAN da wasu Malaman addini irin su Sheikh Ahmed Gumi sun goyi bayan kira da a samar da hanyoyin magance kalubalen Makiyaya a Kasar.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna