Jose Mourinho manajan kungiyar Chelsea, ya tir da ‘yan wasan sa kan rashin yin abin kirki da yin kura kuran da basu kamata ba, a wasansu da suka buga da kungiyar FC Porto, inda Chelsea ta sha kashi da ci biyu da ‘daya.
Kungiyar dai ta shiga gasar wasannin Champion league na wannan kakar wasan da kafar hagu, alokacin da ta sha kashi a Portugal.
‘Dan wasa Andre Andre shine ya baiwa masu karbar bakin kwallon farko, kafin Willian ya jefa ta biyu, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne da taimakon Maicon FC Porto ta zama zakaran wasan.
Manajan Chelsea Jose yace, “ina tunanin wasane mai kyau da kuma manyan kura kurai biyu da basu kamata ayi su ba, wani lokaci zakayi irin wannan kuskure ba tare da samun illarsa ba, amma wannan karon mun ga illarsu.” Ya fadi hakane alokacin da yake magana da manema labarai.
Ya ci gaba da cewa mun kara samun irin wannan kuskuren lokacin da kwallon ta daki karfen raga. Bayan haka kuma ‘yan wasan sun ‘dauki kaddara suka ci gaba da wasansu ba tare da hakan ya damesu ba. ‘yan wasan FC Porto suna da kyau kuma da kwazo.