Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bam Ya Fashe A Kusa Da Muna Garage A Garin Maiduguri


Boko Haram
Boko Haram

An sami fashewar wani bom da missalin karfe tara na dare a kusa da wani gareji da ake kira Muna Garage dake garin Maiduguri, bam din ya kashe dan kunar bakin waken da kuma wasu mutane biyu.

Cikin yan kwanakin nan dai wannan shine karo na hudu da ake samun tashin bam kusa da wannan gareji, ko a makon da ya gabata ma an sami wani dan kunar bakin wake da yayi kokarin kutsawa cikin wannan gareji na Muna Garage amma bai samu nasara ba inda bam din ya tashi da dan kunar bakin waken kadai.

Yanzu haka dai mutane na ci gaba da harkokin kasuwanci a wannan garejin, wani abin al’amari dake faruwa a jihar Borno shine duk wani abu da ya faru idan har aka bada awa daya ko biyu sai duk mutane su koma harkokinsu na yau da kullum. Wanda hakan ke nufin babu wata barazana da zata hanasu neman abincinsu ta hanyar da ta halarta.

Rahotanni dai na cewa akwai wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da suka ajiye makamansu suka mika wuya a jihar Borno, sai dai har yanzu ana jiran bayanai daga gurin jami’an tsaro domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG