Ya tabo batun wani yaro dan shekaru 12 daga California, wanda ya datsa tutocin Amurka dubu arba’in a kan kabarin tsofaffin sojoji da suka mutu a filin daga, a ranar tunawa tsofaffin sojojin ta kasa. Wannan yaro mai suna preston Sharp ya samu girmamawa inda kowa ya mike tsaye ana yaba masa.
Trump yayi kira ga majalisar dattawan ta ba kowane babban jami’in gwamnatinsa ikon yabawa ma’aikata na gari, ta hanyar basu kyauta kuma tayi waje da duk ma’aikatan suke cin amanar jama’a da gaza biyan bukatun Amurkawa.
Shugaban na Amurka ya kuma yayi jawabi a kan yanda Amurkawa ke hada kai a yayin da kasar ta fada cikin wani bala’i. Amma yace
Yace bai wadatu mu hada kai a lokacin bala’I kadai ba, a wannan dare ina kira ga kowanenmu, mu ajiye bambance bambancenmu, mu nemi hanya daya da zata hada kanmu, mu yiwa jama’armu aiki, wannan abu ne mai muhimmanci, saboda sune mutan da suka zabomu mu musu aiki.
Sarfilu Hashim Gumel ya tattauna da Farfesa Yusuf Alhassan mai sharhin a kan harkokin siysar Amurka dake zaune a jihar Missouri a nan Amurka.
Facebook Forum