A washegarin bayyanar labarin tsintuwar gawarwakin mutane 34 a arewacin jamhuriyar Nijer masu bin diddigin al’amuran da suka shafi tafiye tafiyen ‘yan ci ranin nahiyar Afirka sun bayyana cewa tsauraran matakan tsaron da aka dauka akan hanyar Agadez zuwa Algeria shine dalilin dake sanya bakin haure kokarin bullo da sabuwar barauniyar hanya. Saboda haka suka gargadi gwamnatocin kasashen Afirka ta yamm su kara matsa kaimi a ayyukan fadakarwa da samarda aikin yi don takaita wannan matsala dake daukar sabon salo a kulliyaumin.
Wakilinmu Muryar Amurka ya tantauna da SAIDU ABDU wani wanda ya gudanar da bincike akan dalilan yawaitar ‘yan ci ranin Afirka.
Ga cikakken bayani.