Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Da Sa Siyasa A Harin Da Aka Kai Wa Ortom - Buhari


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ayarin gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, amma kuma ya yi gargadin ka da a mayar da lamarin siyasa.

A cikin wata sanarwa daga mataimaki na musamman na shugaban kasa akan sha’anin watsa labarai Malam Garba Shehu, Shugaba Muhammadu Buhari​ ya ce ba za’a lamincewa hare-haren ta’addanci da ake kai wa al’ummomi a jihar, da kuma na baya-bayan nan wanda aka kai wa gwamnan jihar kan sa ba.

Shugaban kasar ya kuma jinjinawa rundunar ‘yan sanda akan aikewa da tawagar kwararrun masu bincike a jihar, inda kuma yayi kira gare su da su yi kokarin bankado dukan masu hannu a kai harin, da kuma hukunta su.

Karin bayani akan: PDP, Shugaba Muhammadu Buhari​, jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.

Bayan jajantawa gwamnati da al’ummar jihar akan lamarin, shugaba Buhari ya yi kiran da kada a sanya siyasa a kan lamarin, inda ya jaddada cewa “kai hari akan dan Najeriya daya, tamkar kai hari ne ga dukan ‘yan kasar.”

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

A ranar Assabar ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan kwamban motocin gwamnan na jihar Benue Samuel Ortom, a kan titin Makurdi zuwa Gboko, sa’adda ya ke kan hanyar ziyartar gona a Tyo.

Tuni dai da kungiyar gwamnonin Arewa suka jajantawa takwaran na su akan lamarin, inda kuma suka dau alkawarin daukar mataki akai.

A bangare daya kuma kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya, sun yi tir da kakkausar murya, da harin da aka kai kan gwamnan na jihar Benue.

Wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin na PDP, kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, sun bayyana harin a matsayin “wani yunkuri na hallaka gwamna Ortom.”

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Haka kuma gwamnonin sun bayyana cewa “duk wani yunkuri na cutar da daya daga cikin mu, tamkar yunkuri ne na cutar da mu baki daya.”

Gwamnonin na PDP sun yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta kara mai da hankali wajen tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayin su a cikin al’umma ba.

XS
SM
MD
LG