Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wajibi Ne Afirka Ta Sake Nazarin Irin Dimokradiyar Data Gada Daga Kasashen Yamma-Obasanjo


Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo (Instagram/ olusegun obasanjo)
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo (Instagram/ olusegun obasanjo)

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro game da yanayin dimokradiya a nahiyar Afirka daya gudana a cibiyar 'Yar’adua dake Abuja a yau Laraba.

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya shawarci kasashen nahiyar Afrika su sake nazarin irin tsarin dimokradiyar da suka gada daga kasashen yammacin duniya.

Obasanjo ya kara da cewar wajibi ne nahiyar Afrika ta gina irin tsarin dimokradiyar daya dace da al'adu da walwalar al'ummarta.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro game da yanayin dimokradiya a nahiyar Afirka daya gudana a cibiyar 'Yar’adua dake Abuja a yau Laraba.

Tsohon Shugaban Najeriyar, wanda ya kasance babban bako mai jawabi a taron, ya bukaci a samar da tsarin dimokradiyar da zai karbu ga kowa.

Ya kuma kalubalanci shugabanin Afirka su kara jajircewa wajen tabbatar da walwalar al'ummarsu.

A cewar Obasanjo, matukar ana son tsarin dimokradiya yayi aiki yadda ya dace a Najeriya dama Afirka baki daya, wajibi ne a gina shi akan tsarin shugabanci nagari da kwararan hukumomi da kuma kyale doka tayi aikinta.

Ya kuma siffanta tsarin dimokradiya da gwamnatin da aka kafa da sahalewar al'umma ta hanyar zaben gaskiya ba tare da ha'inci ba kuma domin jin dadi da walwalar talaka

Taron ya maida hankali ne akan nasarori da kalubale harma da barazanar da tsarin dimokradiya ke fuskanta a nahiyar Afirka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG