Jiya alkhamis, Shugaban Amurka Donald Trump yayiwa manyan ‘yan kasuwar duniya tayi su zo su sarrafa hajojin su a Amurka tare da alkawarin musu rangwamen haraji, amma yayi gargadi cewa duk wanda ya zabi sarrafa hajjojin shi a wata kasa, zai fuskanci haraji mai nauyi da Amurka zata kakabawa kayakin daaka shigo da su daga wata kasa.
“Amurka ta dawo kuma a bude kofarta take tayi kasuwanci,”inji Trump cikin wani sakon bidiyo daga Washington, ga manyan ‘yan kasuwar duniya dake hallartar taron tattalin arzikin duniya a birnin Davos na kasar Switzerland.
“Sako na ga duk ‘yan kasuwa a duniya ita ce: Ku zo ku sarrafa kayakin ku a Amurka, sannan zamu muku saukin harajin da ya fi wanda duk wata kasa a duniya zata muku.”
“Amma idan kuka ki karbar tayin nan wanda shi ne zai fi zama alkhairi gare ku, to a gaskiya, zaku ku biya haraji.”
Kwanaki uku da kama aiki a wa’adin mulkin shi na 2 a fadar White House, Trump yace yana so ya rage yawan harajin da ake biya a Amurka daga kaso 21% zuwa 15%, ko da yake zai bukaci amincewar abokan tafiyar sa na siyasa ‘yan Republican masu rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Mahukuntan sun fara mahawara akan kara haraji da sake fasalin harajin ga mutane da kamfanoni wanda Trump ya tabbatar a 2017 lokacin wa’adin shi na farko.
Trump yayi alkawarta cewa, Amurka zata samarwa Turai iskar gas din da take bukata amma kuma ta ce tarayyar Turai bata kyautatawa Amurka “Tana mata rashin adalci sossai” la’akari da yawan dokokin da ta kakabawa kamfanonin Amurka masu kasunwaci a kasashen kungiyar 27.
Dandalin Mu Tattauna