Lokacin da ya kammala yin sujadar Kirsimati a mijami'ar Bishara dake Sabo Ibadan Fasto Filibus Miyango ya gargadi kiristoci su kaunaci kowa domin haka Allah ya yiwa dan adam. Ya ce yana son ya fadawa mutane musamman kiristoci gaskiya cewa a wannan irin rana ta tunawa da haifuwar Yesu ya kamata kiristoci su yi kauna da juna da wadanda ba kiristoci ba domin haka littafi ya koyas. A rana ta yau ya kamata a yi kyauta, a ci tare a kuma sha tare. Ya ce kome kake dashi ka ba makwafcinka domin littafi bai ce a nuna banbanci ba bisa ga addini. Da kirista da Musulmi da ma wanda bashi da addini duk a kaunaci juna.
Ubangiji ya yi ma dan adam misali da kyautar Yesu. Ya ba duniya Yesu ba tare da nuna banbanci ba. Kyautar ce ta sa wannan bikin na kirsimati inda ake murna ana nuna godiya ga Ubangiji da nuna son juna.
Ita kuma Fasto Debora cewa ta yi a wannan ranar zasu koyawa yara halin rayuwa da zai taimakesu idan sun girma.
An yi bikin lafiya an kuma gama lafiya.
Ga karin bayani.