A yau Kotun Kolin Amurka ta ke shirin sauraron daukaka karar da aka yi akan hukuncin da wadansu kananan kotuna uku suka yanke, dangane da tilastawa shugaba Donald Trump ya fitar da bayyanan harajin da ya ke biya da kuma takardun harkokin kasuwancinsa.
Trump ya kalubalanci umarnin da kwamitoci da dama na majalisar wakilai suka bayar a bara, da kuma wanda wani alkali a birnin New York ya bayar.
Trump ya ki bayyana kadarorin da ya mallaka da harkokin kudinsa, wanda ya sabawa ka’idar da ta bukaci dan takarar shugaban kasa ya bayyana takardun biyan harajinsa.
Wadansu kananan kotuna sun yanke hukunci da ya bukaci Trump ya fitar da bayanan, sai dai har yanzu bai fitar ba, amma ana jiran hukuncin kotun koli.
Lauyoyin Trump sun ce tilas ne ‘yan majalisa su ba da kwararan dalilan da suke bukatar bayanan kadarorin shugaban kasar.
Facebook Forum