Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da wasu jihohin kasar 16 suka shigar a kan antoni janar na tarayya suna kalubalantar halascin dokokin da suka kafa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da wasu hukumomi 2 irinta.
Sauran hukumomin sun hada da ICPC, mai yaki da cin hanci da rashwa da kuma NFIU, mai yaki da laifuffukan da suka shaft kudi.
Kotun kolin ta kori karar ne saboda rashin wadatattun hujjoji.
Da take zartar da hukunci, Mai Shari'a Uwani Abba-Aji tace jihohin sun tafka kuskure da suka ce EFCC da dokar majalisar kasa ta kafa haramtacciyar hukuma ce.
Karar wacce antoni janar-janar na jihohi 16 suka shigar tunda fari, ta nemi a rushe hukumar dake yaki da almundahana.
A yayin da wasu jihohin suka janye daga karar, wasu kuma nema suka yi a sanyasu cikin kunshin masu kara.
Dandalin Mu Tattauna