Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Canada Ta Bada Belin Shugabar Kamfanin Sadarwa Na China


Lisa Duan, wata 'yar Chin tana nuna goyon bayan Huawei
Lisa Duan, wata 'yar Chin tana nuna goyon bayan Huawei

Wata kotun kasar Canada ta bada belin‘yar Chinar nan, shugabar kamfanin sadarwa Meng Wanzhou, yayinda take jira taji ko za a mika ta ga Amurka.

An kama Meng ne a filin saukar jiragen sama a birnin Vancouver bisa ga sammacin kamota da Amurka ta bayar a kan zarginta da take dokokin takunkumin kasuwanci da Iran

Alkali William Ehrcke ya bada belinta a kan kudi dala miliyan bakwai da dubu dari biyar tare da gindaya sharudda a kan Meng. Sharuddan sun ce zata ci gaba da zama a gundumar British Columbia a can Canada, a cikin gidan da mijinta ya mallaka kuma ba zata fita gida daga karfe 11 na dare zuwa karfe shida na safe ba. Za a kuma sanya ido a kan Meng a ko da yaushe.


Meng itace babbar jami’ar kudi a katamfaren kamfanin fasahar sadarwar China na Huawei, da mahaifinta ya kafa kuma yana cikin manyan kamfanonin dake kera wayoyin hannu a duniya. Iyalanta suna da dukiya da ta kai biliyoyin daloli.

A halin da ake ciki kuma, China ta kama tsohon jakadar Canada a China Michael Kovrig a kan wasu dalilai da basu bayyana ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG