Yau Asabar ce shugaban Najeriya Goodluck Jonatahn ya rantsar da sha hudu daga cikin ministocinsa, ya basu umurnin su fara aikin nan take.
Daga cikin ministocin da suka dauki rantsuwar kama aiki yau, 12 tsoffin ministoci ne, kuma zasu ci gaba da aiki a ma’aikatu da suka rike da.Sabbin biyu kuma, Mr. Jonathan yace za’a bayyana ma’aikatu da za’a tura su ranar litinin.
Masu zuba jari ciki da wajen Najeriya suna zura ido kan majalisar ministocin Mr. Jonathan, d a fatan sabuwar majalisar zata kawo sauye sauye da ake bukata ga kasar ta Afirka mafi yawan al’uma.
Cikin wadanda suka sake samun gurabunsu har da wadanda suka riki ma’aikatun stare tsaren kasa, hakar ma’adinai, sadarwa,da shari’a, da kuma ministan harkokin mai.
Shugaba Jonathan ya sake nada ministan ma’aikatar mai, Diezani Alison Maduke yau Asabar, duk da yawan suka da ta samu kan jinkiri zartas da dokar sauye sauye da aka juma ana dako a fannin makamashin kasar, da cin hanci da rashawa yayi wa katutu.