Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Sake Bayyana Sunayen Wadanda Suka Wawushe Dukiyar Kasa


 Lai Mohammed ministan yada labaran Najeriya
Lai Mohammed ministan yada labaran Najeriya

A sanarwar da ministan watsa labarai Lai Muhammad ya sanar ya bayyana karin sunayen 'yan Najeriya da suka tatse arzikin kasar a gwamnatin da ta shude

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta saki kashi na biyu na mutanen da tace sun wawushe baitul-malin kasar kamar yadda jaridun Daily Trust da Premium Times suka ruwaito

A sabon jerin sunayen da ta fitar na wadanda take zargin, gwamnatin tarayyar tace adadin kudi Naira milyan dubu dari da ashirin da shida (watau Bilyan 126) da Dalar Amurka Bilyan 1.5, da fam milyan 5.5 na kudin Ingila ne aka sace ta ofishin mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, kanar Sambo Dasuki mai ritaya.

Wannan matakin ya biyo neman gafara da jam’iyyar PDP tayi, da kuma kalubalantar gwamnatin da jam’iyyar tayi cewa, idan zargin da take yiwa ‘yayan jam’iyyar zamanin gwamnatin da ta shude da gaske ne ta bayyana sunayen mutanen da suka yi kuruciyar bera.

A wannan sabon rukuni na sunayen da ta sake, Ministan yada Labarai Lai Mohammed yace, wadannan adadin da gwamnati ta fitar bai hada da kudaden sayen makamai Dala Biliyan biyu da digo daya da har yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike akai ba.

Na biyu sai tsohuwar Ministar Mai Diezani Alison-Maduke, wacce EFCC take bincike akanta, a lamari daya kadai ana zargin ta yi almubazzarancin Naira Bilyan 23. Banda wannan ana zargin tana da hannu a wani kwangila da aka baiwa wasu

‘yan kasuwa biyu Jide Omokore, da Kola Aluko rijiyoyin mai kudin su ya kai $3 Billion Uku, amma basu biya gwamnati sisin kobo na haraji da wasu hakkokinta ba.

Leftanar Janar Kenneth Minimah ana zarginsa da wawure Naira Bilyan 13.9, EFCC ta gano Naira Bilyan 4.8

Sai Leftanar Janar Azuibuike Ihejirika, Bilyan 4.5, EFCC zuwa yanzu ta kwato milyan 29.

Tsohon babban hafsoshin tsaro na Najeriya Alex Badeh ana zarginsa da wawurar Naira Bilyan 8, zuwa yanzu EFCC ta kwato kudi da kadara da suka kai Bilyan 4.

INde Dikko, wanda shine tsohon Komtrolla Janar na Kastam, ana zarginsa da wawure Bilyan 40, hukuma ta kwato Naira Bilyan 1.1kudi da kadara.

AirVice Marshall Adesola Amosun, ana zargin ya wawushe Naira Bilyan 21.4. An gano Bilyan 2.8 tsabar kudi, kadarori 28 da motoci uku.

Sauran wadanda ake zargi sun hada da tsohuwar Ministan sifiri Stella Oduah Bilyan 9.8. Tsohon Gwamnan jahar Niger Babangida Aliyu, tsohon Gwamnan jahar Flato Jonah Jang da sauran mutane da dama.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG