Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Wadanda Ake Zargi Da Fashin Offa


'Yan fashin da suka kai hari garin Offa na jihar Kwara
'Yan fashin da suka kai hari garin Offa na jihar Kwara

Da take zartar da hukuncin, alkaliyar tace dukkanin shaidun da lauyoyin masu kara suka gabatar sun samesu da laifi.

Mai Shari’a Halima Salman ta babbar kotun jihar Kwara ta samu mutane 5 din da ake zargi da hannu a fashin garin Offa da laifin mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da fashi da makami da kuma kisan kai.

A cewar Mai Shari’ar, hukuncin kowane daga cikin laifuffukan da suka aikata kisa ne.

Al’amarin ya faru ne cikin watan Afrilun 2018.

Game da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, hukuncin ya zartar da zaman gidan kaso na shekaru 3.

Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Ayoade Akinnibosun da Ibikunle Ogunleye da Adeola Abraham da Salahudeen Azeez da Niyi Ogundiran. A yayin da mutum na 6 da ake tuhuma, Micheal Adikwu, ya mutu yayin da yake tsare a kurkuku.

A jawabinsa ga manema labarai, lauyan masu kara yace dalilai da yawa da suka hada da annobar korona da hidimar kasa da aka dorawa mai shari’ar ne suka janyo jan kafa a shari’ar, sannan ya yabawa kotun game da hukuncin.

Sai dai, wakilin lauyan wadanda ake kara, yace zasu daukaka kara akan hukuncin nan ba da jimawa ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG